Litinin 13 Yuli 2026 - 22:46
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (55) | Abubuwan Da Shi'a Da Ahlus Sunna Suka Yi Tarayya A Mahdawiyya

Hauza/ Ahlus-Sunnah sun yi nuni da hakikanin "tunanin Mahdawiyya" a cikin ruwayoyi masu yawa. Duk da cewa a wasu wurare akwai bambance-bambance tsakanin akidarsu da akidar Shi'a, akwai kuma abubuwa masu yawa da suka yi tarayya a cikinsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, ana gabatar muku da jerin bahasosin Mahdawiyya masu taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ma'arifar da suka shafi Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa mai albarka), ga ku masu ilimi da daraja.

Abubuwan da Ahlus-Sunnah da Shi'a suka yi tarayya a bahasin Mahdawiyya

Ahlus-Sunnah sun yi nuni da hakikanin "tunanin Mahdawiyya" a cikin ruwayoyi masu yawa. Duk da cewa a wasu wurare akwai bambance-bambance tsakanin akidarsu da akidar Shi'a, akwai kuma abubuwa masu yawa da suka yi tarayya a cikinsu.

Tabbacin bayyanar da tashin Imam Mahdi (A.F)

Abu na farko da Shi'a da Ahlus-Sunnah suka yi ittifaki a kai shi ne cewa bayyanar da tashin Imam Mahdi (A.F) tabbatacce ne. Wannan batu yana daga cikin tabbatattun akidu na waɗannan mazhabobi biyu; har ma akwai ruwayoyi da dama, ba ma gomomi kaɗai ba har ma ɗaruruwa, game da wannan batu a cikin tushen ruwayoyinsu.

Asalin zuriyar Imam Mahdi (A.F)

Ɗaya daga cikin abubuwan da Shi'a da Ahlus-Sunnah suka kusan yi ittifaki a kai shi ne asalin zuriyar Imam Mahdi (A.F). Shi'a sun bayyana wannan nasaba a fili har zuwa mahaifin Imam Mahdi, amma Ahlus-Sunnah sun yi nuni da wasu sassa daga cikinta kamar haka:

Imam Mahdi (A.S) yana daga Ahlul Baiti kuma daga zuriyar Manzon Allah

Ibn Majah ya ruwaito a cikin Sunan nasa cewa Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«الْمَهْدِی مِنَّا أَهْلَ الْبَیتِ یصْلِحُهُ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ فِی لَیلَةٍ.»

"Mahdi yana daga cikinmu Ahlul Baiti, kuma Allah Maɗaukaki zai gyara al'amarinsa cikin dare guda." (Ibn Majah, Sunan, juzu'i na 2, hadisi na 4085; Kashf al-Ghummah, juzu'i na 2, shafi na 477; Dala'il al-Imamah, shafi na 247)

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«یخرج رجل من أهل بیتی عِنْدَ انْقِطَاعٍ مِنَ الزَّمَانِ وَ ظُهُورٍ مِنَ الْفِتَن یکُونُ عَطَاؤُهُ حثیاً.»

"A ƙarshen zamani lokacin fitowar fitintinu, wani mutum daga Ahlul Baitina zai fito, kuma kyautarsa za ta kasance mai yawa." (Ibn Abi Shaibah, al-Musannaf, hadisi na 37639; Kashf al-Ghummah, juzu'i na 2, shafi na 483)

San'ani ya kawo daga Manzon Allah (SAWA):

«...فَیبْعَثُ اللَّهُ رَجُلًا مِنْ عِتْرَتِی من أَهْلِ بَیتِی...»؛

"Sai Allah Ya aiko wani mutum daga zuriyata, daga Ahlul Baitina..." (San'ani, al-Musannaf, juzu'i na 11, hadisi na 20770; Dabarani, al-Mu'ujam al-Kabir, juzu'i na 10, hadisi na 10213)

Imam Mahdi (A.F) yana daga zuriyar Imam Ali (A.S.)

Daga cikin abubuwan da ruwayoyin Shi'a da Ahlus-Sunnah suka yi ittifaki a kansu akwai cewa Imam Mahdi (A.F) yana daga zuriyar Imam Ali (A.S.).

Suyuɗi ya ruwaito a cikin 'Arf al-Wardi cewa Manzon Allah (SAWA) ya kama hannun Ali (A.S.) ya ce:

«سیخرج من صلب هذا فتی یمْلأ الأَرْضَ قِسْطاً وَ عَدْلاً.»

"Daga zuriyar wannan mutum wani matashi zai fito, wanda zai cika duniya da adalci da daidaito." (Jalaluddin Suyuɗi, al-Hawi lil-Fatawi, Kitab al-'Arf al-Wardi, shafi na 74 da shafi na 88)

Juwayni Shafi'i ya ruwaito daga Ibn Abbas cewa Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«إِنَّ عَلِی بْنَ أَبِی طَالِبٍ علیه‌السلام إِمَامُ أُمَّتِی وَ خَلِیفَتِی عَلَیهَا بَعْدِی وَ مِنْ وُلْدِهِ الْقَائِمُ الْمُنْتَظَرُ الَّذِی یملا الله به الارض عدلا و قسطا کَمَا مُلِئَتْ ظُلْماً وَ جَوْراً...»

"Lallai Ali bn Abi Talib shi ne shugaban al'ummata kuma halifana a kansu bayana. Daga cikin zuriyarsa akwai Al-Qa'im Al-Muntazar, wanda Allah zai cika duniya da adalci da daidaito ta hannunsa kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya."  (Fara'id al-Simtayn, juzu'i na 2, shafi na 327, hadisi na 589; Kamaluddin, juzu'i na 1, shafi na 287, babi na 25, hadisi na 7)

Imam Mahdi yana daga zuriyar Fatima (A.S.)

A cikin ruwayoyi masu yawa na Ahlus-Sunnah an bayyana cewa Imam Mahdi (A.F) yana daga zuriyar Fatima (A.S.).

Ibn Majah ya ruwaito daga Ummu Salama cewa ta ji Manzon Allah (SAWA) yana cewa:

«الْمَهْدِی مِنْ وُلْدِ فَاطِمَةَ.»

"Mahdi yana daga zuriyar Fatima." (Sunan Ibn Majah, hadisi na 086; Sunan Abi Dawud, juzu'i na 4, hadisi na 4284; Nu'aym bn Hammad, al-Fitan, shafi na 375; Hakim, al-Mustadrak, juzu'i na 4, shafi na 557)

Sunan Imam Mahdi (A.S) iri ɗaya ne da na Manzon Allah (SAWA)

Ahlus-Sunnah da Shi'a sun yi ittifaki cewa sunan Imam Mahdi (A.F) iri ɗaya ne da sunan Manzon Allah (SAWA). (Maqdisi Shafi'i, Aqd al-Durar, shafi na 45 da shafi na 55)

Yanayin da zai gabaci bayyanarsa

Wasu sauye-sauyen zamantakewa kafin bayyanarsa sun zo a cikin tushen Shi'a da na Ahlus-Sunnah:

Cikakkiyar yanke ƙauna ta mutane

Dawud bn Kathir al-Raqqi ya ce: "Na ce wa Imam Sadik (A.S): Wannan al'amari (bayyanar) ya yi mana tsawo har ƙirjinmu ya matse... Sai Imam (A.S) ya ce:

"Lokacin da yanke ƙauna daga samun farajinmu ya kai kololuwa... sai mai kira daga sama ya yi kira da sunan Al-Qa'im." (Nu'umani, al-Ghaybah, shafi na 186, hadisi na 29)

Manzon Allah (SAWA) ya ce wa Imam Ali (A.S):

"Ya Ali! Bayyanar Mahdi za ta kasance ne lokacin da birane suka canza, bayin Allah suka raunana kuma suka yanke ƙauna daga faraji da bayyanar Mahdi; a lokacin ne Mahdi Al-Qa'im daga zuriyata zai bayyana." (Qanduzi, Yanabi' al-Mawaddah, shafi na 528; duba kuma: al-Bayan fi Akhbar Sahib al-Zaman, shafi na 42, hadisi na 21; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 92)

Yawaitar zalunci

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«لَوْ لَمْ یبْقَ مِنَ الدُّنْیا إِلَّا یوْمٌ لَطَوَّلَ اللَّهُ ذَلِکَ الْیوْمَ حَتَّی یبْعَثَ رَجُلًا مِنْ أَهْلِ بَیتِی یمْلَأُ الْأَرْضَ عَدْلًا وَ قِسْطاً کَمَا مُلِئَتْ ظُلْماً وَ جَوْراً...»

"Ko da rana daya ce ta rage a duniya, Allah zai tsawaita wannan ranar har sai Ya aiko wani mutum daga Ahlul Baitina wanda zai cika duniya da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya."  (Sunan Abi Dawud, hadisi na 4282)

Alamomin bayyanarsa

A cikin tushen ruwayoyin Shi'a an ambaci wasu abubuwan da za su faru nan gaba da sunan alamomin bayyanar. An raba su zuwa tabbatattu da waɗanda ba tabbatattu ba, kuma wasu daga cikinsu sun zo a cikin tushen Ahlus-Sunnah.

a. Kira daga sama

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

"A watan Muharram za a ji wani kira daga sama da wannan ma'ana: Zaɓaɓɓen Allah shi ne wane (Mahdi), saboda haka ku saurari maganarsa kuma ku bi shi." (Nu'aym bn Hammad, al-Fitan, shafi na 93; Aqd al-Durar, shafi na 79, 83, 99; duba kuma Fara'id al-Simtayn, juzu'i na 2, shafi na 316; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 73)

Imam Ali bn Abi Talib (A.S) ya ce:

"Lokacin da mai kira daga sama ya yi kira cewa gaskiya tana tare da Alu Muhammad (SAWA), a lokacin ne Mahdi zai bayyana." (Ja'afar bn Muhammad Ibn al-Munadi, al-Malahim, shafi na 196, hadisi na 143)

Imam Sadik (A.S) ya ce:

«النِّدَاءُ مِنَ الْمَحْتُوم...»

"Kira daga sama yana daga cikin alamomi tabbatattu."  (Nu'mani, al-Ghaybah, h11)

b. Sufyani

Wata alama ta bayyanar Mahdi Muntazar ita ce fitowar wani mutum mai suna Sufyani. A cikin hadisan Shi'a an jaddada tabbacin faruwarsa. (duba: Nu'umani, al-Ghaybah...)

A wasu hadisan Ahlus-Sunnah ma an bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin alamomin bayyanar Imam Mahdi (A.F). (al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 80; Aqd al-Durar, shafi na 76; duba kuma Kanz al-'Ummal, juzu'i na 11, shafi na 273)

c. Kifewar ƙasa a Bayda

Kalmar "Khasf" na nufin nutsewa ko shige wa cikin ƙasa, kuma "Bayda'" sunan wani wuri ne tsakanin Makka da Madina.

Ma'anar wannan alama ita ce, Sufyani zai nufi Makka da runduna mai yawa domin yaƙi da Imam Mahdi (A.F). A tsakanin Makka da Madina, a wani wuri da ake kira Bayda', za su nutse cikin ƙasa ta hanyar mu'ujiza.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«...فَیبْعَثُ إِلَیهِ جَیشٌ من الشام حَتَّی إِذَا کَانُوا بِالْبَیدَاءِ خُسِفَ بِهِمْ...»؛

"Za a aiko masa da wata runduna daga Sham; idan sun isa Bayda', sai a nutsar da su cikin ƙasa." (San'ani, al-Musannaf, juzu'i na 11, sh.'afi na 371)

(duba kuma: Dabarani, al-Mu'ujam al-Awsat, juzu'i na 2, shafi na 35; Kanz al-'Ummal, juzu'i na 11, shafi na 277, hadisi na 31513; al-Bayan, shafi na 44, hadisi na 23; Aqd al-Durar, shafi na 80; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 71)

d. Kisan Nafs Zakiyya

Daya daga cikin alamomi tabbatattu, wanda kuma wasu tushen Ahlus-Sunnah suka ambata, shi ne kashe wani mutum mai tsarki kuma marar laifi a tsakanin Rukni da Maqam, gab da tashin Imam Mahdi (AS). (Ibn Abi Shaibah, al-Musannaf, juzu'i na 8, shafi na 679; Kanz al-'Ummal, juzu'i na 11, shafi na 277; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 78)

Abubuwan da suka shafi bayyanar Imam Mahdi (A.S)

i. Shirya al'amarin bayyanarsa cikin dare guda

Ruwayoyi sun nuna cewa al'amarin bayyanar Imam Mahdi (A.F) za a shirya shi cikin dare guda. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da Shi'a da Ahlus-Sunnah suka ambata. (al-Bayan, shafi na 31, hadisi na 11; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 69; Aqd al-Durar, shafi na 210)

ii. Wurin bayyanarsa

An kawo ruwayoyi masu yawa game da inda bayyanar Imam Mahdi (A.F) za ta fara da kuma inda sahabbansa na musamman za su hadu da shi. Abin da ya haɗa waɗannan ruwayoyi shi ne cewa bayyanarsa za ta fara daga Makka. (Nu'umani, al-Ghaybah, shafi na 313, hadisi na 4 da shafi na 315, hadisi 9; Aqd al-Durar, babi na 2, shafi na 56)

Kuma bisa ga ruwayoyi masu yawa, za ta fara ne daga gefen Ka'aba.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

"Wasu jama'a daga Iraki da manya daga Sham za su zo wurin Mahdi kuma za su yi masa mubaya'a tsakanin Rukni da Maqam..." (Nu'aim bn Hammad, al-Fitan, sashe na huɗu, shafi na 242, hadisi na 950)

Haka kuma ya ce:

"...Za a yi mubaya'a ga Mahdi tsakanin Rukni da Maqam." (Aqd al-Durar, babi na 2, shafi na 56)

iii. Saukar mala'iku domin taimakon Imam Mahdi (A.F)

Daya daga cikin abubuwan da Shi'a da Ahlus-Sunnah suka yi tarayya a kansu shi ne saukar mala'iku domin taimakon Imam Mahdi (A.F) lokacin bayyanarsa. (Aqd al-Durar, shafi na 46, 117, 185; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 88; al-Bayan, shafi na 84, hadisi na 53)

iv. Saukar Annabi Isa (A.S) da yin salla a bayan Imam Mahdi (A.F)

Daya daga cikin manyan abubuwan da za su faru a zamanin bayyanarsa shi ne dawowar Annabi Isa (A.S). An ambaci wannan a cikin ruwayoyi masu yawa.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«یلتفت المهدی و قد نزل عیسی بن مریم کانما یقطر من شعره الماء، فیقول المهدی: تقدم، وَصلِّ بالناس فیقول عیسی بن مریم: انما اقیمت الصَّلاة لک فیصلی عیسی خلف رجل من ولدی...»

"Mahdi zai ga Isa bn Maryam ya sauko kamar ruwa na ɗiga daga gashinsa. Sai Mahdi ya ce masa: Ka gabata ka jagoranci salla. Sai Isa ya ce: An tsayar da salla ne dominka. Sai Isa ya yi salla a bayan wani mutum daga zuriyata." (Aqd al-Durar, shafi na 292; Kashf al-Ghummah, juzu'i na 3, shafi na 278)

Haka kuma ya ce:

"...Jibrilu ya zo wurina ya ce: Ya Muhammad! Allah Maɗaukaki Ya zaɓi abubuwa bakwai daga Banu Hashim... kuma daga cikinku akwai Al-Qa'im wanda Isa bn Maryam zai yi salla a bayansa." (al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 50, hadisi na 10)

Imam Sadik (A.S) ya ce:

«...وَ ینْزِلُ رُوحُ اللَّهِ عِیسَی ابْنُ مَرْیمَ فَیصَلِّی خَلْفَهُ...»

"Ruhullah Isa bn Maryam zai sauko kuma zai yi salla a bayansa." (Kamaluddin, juzu'i na 2, shafi na 330, hadisi na 16)

Siffofin gwamnatin Imam Mahdi (A.F)

- Yaɗa adalci

Bisa ga ruwayoyi masu yawa, adalci da daidaito suna daga cikin manyan manufofin tashin Imam Mahdi (A.F). Wannan ya zo ba kawai a cikin ruwayoyin Shi'a ba, har ma a cikin ruwayoyi masu yawa na Ahlus-Sunnah. (Musannaf Ibn Abi Shaibah, hadisi na 19484; Sunan Abi Dawud, hadisi na 4282; al-Mu'ujam al-Kabir, hadisi na 10219 da hadiai na 10220)

- Wadata da jin daɗin rayuwa ga kowa

Daya daga cikin siffofin gwamnatin Imam Mahdi (A.F) shi ne wadatar rayuwa ga jama'a baki ɗaya. Wannan ma ya zo a cikin ruwayoyin Shi'a da Ahlus-Sunnah. (al-Bayan, shafi na 43, hadisi na 22; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 71; Aqd al-Durar, shafi na 195)

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«یکون فی امتی المهدی ... تعیش امتی فی زمانه عیشاً لم تعشه قبل ذلک.»

"Mahdi zai kasance a cikin al'ummata... Al'ummata za su rayu a zamaninsa irin rayuwar da ba su taɓa rayuwa irinta ba." (Ibn Abu Shaibah, Al-Musannaf juzu'i na 7, hadisi na 19484)

Haka kuma ya ce:

«یکُونُ فِی أُمَّتِی الْمَهْدِی ... یتَنَعَّمُ فِیهِ أُمَّتِی نِعْمَةً لَمْ یتَنَعَّمُوا مِثْلَهَا قَطُّ.»

"Mahdi zai kasance a cikin al'ummata... A zamaninsa al'ummata za su more wata ni'ima da ba su taɓa samun irinta ba." (Ibn Majah Qazvini, Sunan, hadisi na 4083; Ali Bin Musa Arbili, Kashf al-Ghumma fi ma'arifat al-A'immah, juzu'i na 3, shafi na 257)

Gamsuwar jama'a da gwamnatin Imam Mahdi (A.F)

Dukkan mutane bayan bayyanarsa da kuma lokacin mulkinsa za su kasance cikin cikakkiyar gamsuwa da shugabancinsa. Wannan ma ya zo a cikin ruwayoyin Shi'a da na Ahlus-Sunnah. (San'ani, al-Musannaf, hadisi na 20770; al-Bayan, shafi na 42, hadisi na 21; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 69; Aqd al-Durar, shafi na 73; Fara'id al-Simtayn, juzu'i na 2, shafi na 310, hadisi na 561)

Tsaro na gaba ɗaya

Daya daga cikin manyan siffofin al'ummar zamanin bayyanarsa shi ne cikakken tsaro a duk faɗin duniya. (Aqd al-Durar, shafi na 207)

Imam Baƙir (A.S) ya ce:

"Wallahi! [Sahabban Mahdi] za su yi yaƙi har sai ya zama Allah Shi kaɗai ake bautawa ba tare da haɗa Shi da wani ba; har ma tsohuwa mai rauni za ta yi tafiya daga wannan gefen duniya zuwa ɗayan ba tare da wani ya cutar da ita ba." (Tabarani, al-Mu'ujam al-Kabir, juzu'i na 8, shafi na 179)

Jin wadatuwa a zukatan mutane

Daya daga cikin halayen mutane a zamanin bayyanarsa shi ne jin wadatuwa.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«أُبَشِّرُکُمْ بِالْمَهْدِی ... وَ یمْللاً اللَّهُ قُلُوبَ أُمَّةِ مُحَمَّدٍ غِنًی...»؛

"Ina yi muku bushara da Mahdi... Lokacin bayyanarsa Allah zai cika zukatan al'ummar Muhammad (SAWA) da wadatuwa." (Musnad Ahmad, j3, shafi na 37; Aqd al-Durar, babi na 8, shafi na 219) (duba kuma: al-Bayan, shafi na 61, hadisi na 38; al-Hawi lil-Fatawi, shafi na 76)

Rinjayen Musulunci a kan sauran addinai

Daya daga cikin abubuwan da Shi'a da Ahlus-Sunnah suka yi tarayya a kansu shi ne rinjayen addinin Musulunci a kan sauran addinai a zamanin bayyanarsa. (Aqd al-Durar, shafi na 95)

Duniya baki ɗaya za ta kasance ƙarƙashin gwamnatin Imam Mahdi (A.F)

Ruwayoyi masu yawa sun jaddada cewa gwamnatin Imam Mahdi (A.F) za ta mamaye duniya baki ɗaya.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«... یبایع له الناس بین الرکن و المقام، یردالله به الدین و یفتح له فتوحاً، فلایبقی علی وجه الارض الا من یقول: لااله الا الله.»؛

"Mutane za su yi masa mubaya'a tsakanin Rukni da Maqam. Allah zai mayar da addini ta hannunsa kuma Ya ba shi nasarori, har ba wanda zai rage a doron ƙasa sai wanda yake cewa: 'La ilaha illa Allah.'" (Aqd al-Durar, babi na biyu)

Imam Sadik (A.S) ya ce:

«إِذَا قَامَ الْقَائِمُ لا تَبْقَی أَرْضٌ إِلا نُودِی فِیهَا شَهَادَةُ أَنْ لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَ أَنَّ مُحَمَّداً رَسُولُ اللَّهِ»؛

"Lokacin da Al-Qa'im ya tashi, babu wata ƙasa da za ta rage sai an yi kira a cikinta da shahadodi biyu: 'Ashhadu an la ilaha illa Allah wa anna Muhammadan Rasulullah.'" (Tafsir al-Ayyashi, juzu'i na 1, shafi na 207, hadisi na 81)

Ya kamata a lura cewa game da siffofin jikin Imam Mahdi (A.F) ma akwai ruwayoyi masu yawa da suka haɗa tushen Shi'a da na Ahlus-Sunnah.

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ciro daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat", wanda Khodamurad Salimiyan ya rubuta, tare da ɗan gyara kadan 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha